On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Tura 'Yan sanda Dubu 21 Jihar Osun, Domin Tabbatar Da Tsaro A Yayin Zaben Gwamna

JAMI'AN YANSANDA

Sufeton Rundunar Yansanda ta kasa, Usman Alkali Baba, Yace za’a tura jami’an yansanda dubu 21 domin tabbatar da tsaro a yayin zaben gwamnan jihar Osun, na ranar 16 ga watan da muke ciki da za’a yi.

Alkali wanda ya baiyana haka a birnin Osogbo yayin wani taron masu ruwa da tsaki, wanda Hukumar Zabe ta  kasa, mai zaman kanta ta shirya, Yace  ba’a tura  jami’an yansandan domin cin zarafin  jihar ba, sai dai kawai domin kawar da dukkanin wasu  miyagun aiyuka  da ka iya kawo cikas wajen gabatar da zaben.

Kazalika yace, jami’an  yansandan zasu bayar da cikakken tsaro, tare da kare masu yin zabe  da  kuma kayan da za’a yi amfani dasu wajen yin zaben.

Bugu da kari, Sufeton rundunar yansandan  ta kasa, Ya baiyana cewa jami’an tsaron da za’a tura  sun samu horo na musamman sannan kuma sun san dokokin  da  gwamnati ta shimfida, sannan kuma ya bada tabbacin cewa jami’an yansandan zasu kauracewa tsoma  kansu cikin harkokin siyasa.