On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Za'a Yiwa 'Yansanda Masu Bada Hannu Akan Titi Karin Girma

Mai bada hannu

Sufeton rundunar ‘yansanda ta kasa Usman Alkali Baba, Ya bada umarnin tantance kwazon jami’an rundunar dake aikin bada hannu akan titina da kula da zirga-zirgar ababen hawa, domin yi masu karin girma zuwa matsayi na gaba.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Olumiyiwa Adejobi ya fitar a jiya,  Ta ce  aikin tantacewar  wani bangare ne  na  yiwa jami’an karin girma.

Ya ce  sufeton yansandan na kasa  ya bada umarnin daga  likafar  jami’an  yansandan  masu aikin bada  hannu  da suka dace bisa  la’akari da kwazonsu wajen aiki, da kuma shaidar karatu da suke da shi, zuwa  matsayi na gaba.

Kakakin ‘yansandan na kasa, Ya ce  wannan wani bangare ne na kokarin da rundunar  ta take na samarwa da  jami’an ta  cigaban da ake bukata.