On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Zababben Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Gida Najeriya

TINUBU

Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ya ce Lafiyarsa Kalau sannan kuma a shirye yake wajen tafiyar da harkokin mulkin kasar nan,Gabanin rantsar dashi a matsayin shugaban taraiyyar kasar nan.

Tinubu ya baiyana haka ne  jim kadan bayan dawowarsa gida Najeriya bayan shafe kimanin wata daya  yana hutu a birnin Paris na kasar Faransa.

A lokacin da yake yiwa manema Labarai jawabi a filin jirgin sama na  Abuja, Tinubu ya musanta rahotannin dake cewar ya fita kasar nan ne domin a duba lafiyarsa saboda wata rashin lafiya  da ba’a baiyana ba.

Dangane da tsare-tsaren da yake yiwa kasar nan kuwa,Tinubu  ya  ce a yanzu haka  yana tattaunawa  tare da neman shawara  kan yadda za’a samu nagartacciyar gwamnati da zarar an rantsar dashi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan gobe.

Zababben shugaban kasar  ya wallafa hotonsa a shafinsa na Tuwita inda  ya baiyana cewar yana farin ciki da dawowarsa gida Najeriya.