On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Zababben Shugaban Najeriya Tinubu Da Kashim Shetima Sun Karbi Lambar Girmamawa Ta GCFR Da GCON

Zababben shugaban kasa, Tinubu da mataimakinsa zababben shugaban kasa, Kashim Shetima sun karbi lambar girmamawa ta GCFR da GCON.

Daga yanzu za a rika  kiran Tinubu da babban kwamandan Askarawan tarayyar Najeriya GCFR sai Shattima da ya zama  mai lambar GCON.

A yayin bikin dake gudana  a halin yanzu a babban birnin tarayya Abuja, za a mika kundin karbar mulki ga sabbin zababbun shugabannin.