On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

ZABEN 2023 - Banyi Mamaki Ba Janyewar Yakin Neman Zaben Atiku A Jihar Rivers - Wike

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike yace bai yi mamaki ba yadda kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya soke taron da aka shirya yi a jihar.

Gwamna Wike ya bayyana haka ne a taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP a karamar hukumar Akuku-Toru, ranar Litinin.

Gwamna Wike ya kuma kalubalanci Abiye Sekibo da ya bayyana wanda ya kashe tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP Cif AK Dikibo na Kudu maso Kudu da kuma Gospel Biobele.

Tun da farko, Yayin da yake bayyana dalilin soke taron a jiya, shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Sanata Lee Maeba yace hukumomin tsaro ba su iya tabbatar da isasshen tsaro a jihar.

Sanata Maeba ya kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya yi tsaiwar daka akan hukumomin tsaro su kasance masu aiki cikin kwarewa da rashin son zuciya wajen gudanar da ayyukansu a lokacin da kuma bayan zabukan 2023.