On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

ZABEN 2023: Buhari Ya Roki 'Yan Najeriya Su Fito Su Zabi 'Yan Takara Da Suke Muradi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake rokon ‘yan Najeriya da su fito  zaben 2023 domin kada kuri’a ga  ‘yan takarar da suke muradi.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ‘yan kasar a safiyar yau.

Shugaban ya amince da cewa sabon tsarin hada-hadar kudi da CBN ya aiwatar ya taimaka matuka wajen rage tasirin kudi a harkokin siyasa.

A cewarsa, wannan wani mataki ne mai kyau na ficewa daga tsohon tsari zuwa sabo, kuma yana wakiltar wani gagarumin mataki da wannan gwamnati ta dauka, na kafa ginshikin gudanar da sahihin zabe.