On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

ZABEN 2023 : Gwamna Matawalle Na Jihar Zamfara Ya Rungumi Kaddara

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya amince da shan kaye a zaben gwamna na 2023 da aka kammala.

Gwamnan ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar PDP Dauda Lawal Dare.

A wani sakon murya da ya aikewa al’ummar jihar, Matawalle yace dole ne shi kansa da dukkan magoya bayansa su mika wuya ga abunda  Allah madaukakin sarki ya tsara domin da yardarsa ne al’amura ke faruwa.

 

Tunda farko hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC a  jihar Zamfara ta ayyana Dauda Lawal Dare a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Dauda Lawal ya samu ƙuri'u 377,726 - inda ya yi nasara a kan gwamna mai ci Bello Muhammad Matawalle wanda ya samu ƙuri'u 311,976.

An dauki tsawon lokaci ana tattara sakamakon zaɓen sanadiyyar jinkiri da aka samu, an  kuma sace jami'an tattara sakamakon zaɓe a kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin jihar, daga ƙaramar hukumar Maradun, sai dai daga bisani sun samu 'yanci.