On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

ZABEN 2023 : Ina Bukatar Tsabar Kudi Naira Miliyan 70 Domin Hidindimun Zabe - Alhassan Doguwa

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, yace yana bukatar tsabar kudi naira miliyan 70 domin yin hidindimunsa na  babban zabe kamar yadda doka ta tanada.

Doguwa yayi magana ne a ranar Alhamis bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta villa dake Abuja.

Ya ce ba tare da tsabar  kudin  ba, wadanda ke neman samun kujeru a majalisar dokokin kasarnan za su sha wahala.

Doguwa dai yana magana ne akan kashe kudaden da masu neman kujeru a majalisar dokokin kasar nan kamar yadda sashe na 88 (4) na dokar zabe ya tanada, sai dai kuma dokar ba ta bayyana cewa dole ne kudaden su kasance tsaba  ba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 37°C | Low: 23°C