On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

ZABEN 2023:: INEC Ta Ayyana Ahamadu Fintiri Na Jam'iyyar PDP Amatsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta Ayyana Ahmadu Umaru Fintiri na Jam’iyyar PDP amatsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa na 2023.

Babban Jami’in tattara sakamakon zaben Ferfesa Mele Muhammad, yace Fintiri ya samu kuri’u dubu 430 da 861.

Haka kuma Aishatu ‘Dahiru Binani ta APC wadda tazo ta biyu ta samu jimillah kuri’u dubu 396 da  788.

Hakan ya biyo bayan kammala tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Adamawa, bayan ta dakatar da shi a ranar Lahadi.

Matakin ya zo ne bayan wani taron da kwamishinonin zaɓe na ƙasa suka gudanar ranar Talata a Abuja.

Jimilla a zaben cike gibi da aka gudanar ranar asabar da ta gabata 15 ga watan Afrilu.