Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta amince ne kawai da 'yan takarar da shugabancin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) karkashin jagorancin Sanata David Mark ya gabatar, tare da tabbatar da cewa bangaren ya riga ya tsayar da 'yan takara 471 domin mukaman zabe gabanin babban zaben shekarar 2027.
Kwamishinan INEC na Kasa, Mohammed Haruna, ya ce hukumar ta bai wa bangaren David Mark damar shiga manhajar gabatar da sunayen 'yan takara bayan hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da shugabancinsa, yana mai cewa dayan bangaren ba shi da hurumin doka na gabatar da 'yan takara. Ya ce, "Eh, mun bai wa bangaren David Mark damar shiga ne bisa hukuncin Kotun Koli na baya-bayan nan da ya tabbatar da shugabancinsa a jam'iyyar, kuma tun daga lokacin bangaren ya gabatar da mafi yawan 'yan takararsa, jimilla 471 – 'yan takarar shugaban kasa (2), na Majalisar Dattawa (109) da na Majalisar Wakilai (360). "Sai dai kotun ba ta ce mu karbi duk wata takarda da dayan bangaren ya gabatar ba, musamman ganin cewa ya rasa daukaka karar da ya shigar domin neman a amince da shi." Sai dai ADC ta bukaci a gudanar da bincike tare da gurfanar da shugaban bangarenta, Nafiu Gombe, bayan INEC ta bayyana cewa ikirarin da ya yi na cewa ya loda sunayen 'yan takarar jam'iyyar domin zaben 2027 ta hanyar manhajar gabatar da sunayen 'yan takara ta hukumar ba gaskiya ba ne. Sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Talata ta biyo bayan karin hasken da INEC ta yi cewa ba ta bai wa Bala lambar shiga manhajarta ta musamman ba, kuma Kwamitin Zartarwa na Kasa karkashin jagorancin David Mark ne kadai hukumar ta amince da shi. Da take mayar da martani kan bayanin INEC, ADC ta yaba da matsayin hukumar tare da zargin Bala da kokarin yaudarar 'yan Najeriya. Jam'iyyar ta ce lamarin ya wuce sabanin siyasa, kuma yanzu ya koma yunkurin yaudarar jama'a. Sanarwar ta ce, "Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) na maraba da gaggawar bayanin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar, wanda ya tabbatar karara cewa takardar da Mista Nafiu Bala ya yada yana ikirarin cewa ya samu lambar shiga ta hukumar kuma ya loda sunayen 'yan takara a madadin ADC domin babban zaben 2027 jabun takarda ce, kuma ikirarin gaba daya karya ne."
Comments
Add a comment