On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Zaben Raba Gardama Na Ficewa Daga Najeriya Ne A Gabanmu Ba Zabukan 2023 Ba - IPOP

Yayin da ya rage kwanaki 10 kacal a gudanar da babban zaben shekarar 2023, masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOP sun dage cewa ba su da sha’awar zaben, sai dai abin da suka sa a gaba shi ne ranar zaben raba gardama na ficewa daga Najeriya.

Wata sanarwa da kakakin kungiyar ta IPOB, Emma Powerful, ya fitar ta tabbatar da matsayin haramtacciyar kungiyar a ranar Litinin.

Sai dai sanarwar ta nesanta kanta daga hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin INEC a wasu yankunan Kudu maso Gabas.

Har ila yau, ta musanta wata sabon jita-jita game da umarnin zama-a-gida a yankin.