On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Zaman Lafiyar Jihar Kano Da Arewa Yafi Komai Dadi - Garkuwan matasan Arewa.

Shugaban kungiyar matasan jihar Kano masu rajin samar da cigaba a bangaren siyasa Ambasada Rabiu Abubakar Tumfafi (Garkuwan matasan Arewa) ya yi Jan hakali ga daukacin  matasan Jihar Kano da su kaucewa shiga duk wani al'amari da ka iya kawo tunzuri ko tayar da tarzoma.

Garkuwan matasan Arewacin Najeriya, ya kara da cewa  samar da zaman lafiyar Al'umma da kuma bunkasar kasuwancin su na din_din_din a jahar Kano nada matukar muhimmanci, saboda haka kawo hargitsi ba zai amfanar da komai ba sai koma baya.