On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Kana Cikin Rudanni: Martanin Atiku Bayan Tinubu Ya Zargi Yan Adawa da Haddasa Yunwa

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci al’ummar arewacin Najeriya da su sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a karo na biyu a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa shugaban ƙasar ya cancanci goyon bayan yankin saboda irin taimakon da ya bayar a baya ga shugabannin siyasar Arewa.

Shettima ya bayyana hakan ne jiya a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna, inda ya kuma buƙaci masu zaɓe su marawa ’yan takarar jam’iyyar baya a dukkan matakan mulki, yana mai nuni da goyon bayan da Tinubu ya bai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a matsayin dalilin da ya sa ya kamata Arewa ta rama masa da goyon bayan sake zaɓensa.

A nasa jawabin a wajen taron, Shugaba Bola Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a Najeriya, yana mai cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalolin da ake dangantawa da ita, tare da alƙawarin kawo wadata ga al’ummar ƙasar idan suka sake zaɓensa, yana mai tabbatar wa magoya bayansa cewa ba za su yi nadamar ba shi wa’adi na biyu ba.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga kalaman Tinubu, inda ya zarge shi da ƙoƙarin ɗora wa ’yan adawa alhakin matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta, yana mai cewa dole ne gwamnatin ta yi bayani kan irin ayyukan da ta gudanar gabanin zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa manufofinsa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya bayyana kalaman shugaban ƙasar a matsayin abin da ya kira ko dai ruɗani ko kuma larurar mantuwa akan abubuwan da ke faruwa a kasar

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 36°C | Low: 16°C