On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Zamu Cigaba Da Samar Da Sabbin Kwasa-Kwasai Domin Bunkasa Sarrafa Amfanin Gona A Najeriya - Dr Gwaram

Shugaban Kwalejin Fasahar  sarrafa Amfanin Gona ta tarayya dake jihar Kano, Dr Muhammad Yusha’u Gwaram, ya bayyana aikin noma a matsayin ingantacciyar hanya wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Dr Gwaram ya bayyana haka ne  yayin da a karon farko kwalejin ta gudanar da bikin rantsar da  sabbin dalibai da za su yi karatu a fannoni  daban-daban na kwalejin.

Kazalika Ya yi gargadin cewa kwalejin da su maida hankali a karatunsu domin zama ‘yan kasa da zasu jagoraci samar da sauyi da dogaro da kai da wadata Najeiya da Abinci.

FCAPT

Da take zantawa da wakilinmu  Kamaluddeen Mohammad darakta sashin tuntuba a kwalejin, Hajiya Aishatu Maiwada Ahmad, ta  bayyana cewa kimanin Dalibai 200 akayi bikin rantsarwa, tana mai jaddada cewa kwalejin ta bullo da tsarin karatu na wurin gadi  nufin karfafa gwiwar masu sha’awar aikin gona.

Hajiya Aisha Maiwada Ahmad ta kuma gargadi daliban da su nisanta kansu daga kungiyoyin asiri da sauran nau'o'in laifuka dake  barazana ga zamantakewar jama'a saboda makarantar  ba za ta amince da kowane nau'i rashin ‘Da’a ba.

Shima, Babban daraktan cibiyar wayar da kan jama’a da rashin tabbatar da adalci, CAJA Comrade Kabiru Sa’idu Dakata ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun karuwar cin zarafi a manyan makarantu, sai dai ya dora alhakin wasu matsalolin akan  dalibai da ke gayyatar cin zarafi.

Ya bukaci daliban da su kai rahoton duk wani cin zarafi  yana mai kira ga daliban suma su rika sanya tufafin da suka dace, yayinda  ya yabawa hukumar kwalejin ta aikin gona bisa daukar matakan da suka dace da kuma shirya bikin rantsar da daliban na farko.