On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Kama Wani Soja Dake Bawa Masu Garkuwa Da Mutane Hayar Bindiga A Abuja

SOJOJI

Jami’an tsaro na farin kaya sun kama wani soja dake aiki a bataliyar Muhammadu Buhari dake Tungan Maje a birnin taraiyya Abuja, bisa zarginsa da sayarwa masu garkuwa da mutane Bindigogi da kuma basu hayar ta.

A karshen makon jiya ne, jami’an tsaro na farin kaya suka  gudanar da sumamen wanda ya basu nasarar kama shi a kusa da  wani wurin shakatawa na Dan kogi dake Zuba hadin gwiwa da jami’an sintiri na yankin.

Wata majiya daga jami’an sintirin ta fadawa manema Labarai cewa wanda ake zargin  a karon farko,Sojan da ake zargi ya bawa masu garkuwar hayar bindiga domin yin garkuwa da mutane akan kudi naira dubu 300 , Sannan kuma daga bisani sun sake nemansa inda ya bukaci su bashi dubu  200, wanda masu garkuwar suka yi ikirarin cewa sun bashi kudin, amma  daga bisani yaki basu bindigar.

DSSS  2

JAMI'AN TSARO NA DSS

Majiyar ta baiyana cewa masu garkuwar wadanda suke a hannun hukumar DSS, sune  suka kwarmata sojan, wanda yake kan shirin samar masu da Bindiga kirar  AK 47 akan kudi naira milyan 3 kafin dubunsa ta cika.