On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Kone Sama Da Tan 15 Na Miyagun Kwayoyi A Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, data magance matsalolin cikin gida take kawo mata tarnaki wajen yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Gwamnan ya yi wannan roko ne  ta bakin shugaban Ma’aikatansa, Shehu Sagagi a  yayin kona Tan 15 da digo 7 na miyagun kwayoyi da  hukumar ta NDLEA ta  yi.

Ya  ce  samun wasu mutane a cikin hukumar  da ke yiwa hukumar zagon kasa ta hanyar hada baki da masu dillancin miyagun kwayoyi, na komar da kokarin gwamnati baya  na yaki da matsalar.

Haka zalika  gwamnan ya jaddada  kudirin jihar nan na yaki da matsalar shaye-shaye  ta hanyar  samar da cibiyoyin koyar da sana’oi domin  sauya  matasa  daga kan wannan   halaiyya.