On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Buhari ba zai iya magance matsalolin Najeriya ba - Kungiyar Dattawan Arewa

A cewar  sanarwar da kungiyar  ta fitar, matakan da gwamnati ke dauka

Kungiyar  Dattawan Arewa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus  daga kan kujerarsa  sakamakon gazawa  wajen samar da cikakken tsaro a Najeriya.


Kungiyar  ta  yi  wannan bukata ce  ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinta Dr Hakeem  Baba –Ahmed.


Kungiyar  Dattawan Arewan ta  baiyana  bacin ranta  dangane  da yadda  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwashe  kimanin shekaru 7 akan karagar mulki, amma har yanzu an  gaza  magance  matsalolin rashin tsaro da suka addabi Najeriya.

A cewar  sanarwar da kungiyar  ta fitar, matakan da gwamnati ke dauka a halin yanzu  basu yi daidai da yanayin  magance  matsalolin rashin tsaro da ake  fuskanta   ba.