On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

‘Dan majalissa ya tsallake Rijiya da baya - Jos ta Arewa da Bassa

Koda yake dukkansu sun tsallake rijiya da baya...

Sabon zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilai, Musa Agah Avia ya tsallake rijiya da baya a wani harin kwantan bauna da ‘yan bindiga suka kai musu a daren ranar Talata. 
A wata sanarwa dauke da sahannun sakataren kungiyar ci gaban Irigwe na kasa, Danjuma Dickson Auta, yace dan majalisar tare da matarsa da ‘ya’yansa da kuma mataimakinsa da direban sa sun fuskanci harin  kwanton bauna a wani wuri dake masarautar Miango a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato. 
Koda yake dukkansu sun tsallake rijiya da baya, amma motar ta samu harbin bindiga yayin da direban bisa ga dukkan alamu ya yi jarumta da motar yayin da maharan ke ta harbe-harbe ba kakkautawa.