On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Jami'an Tsaro Na Shirin Tunkarar 'Yan Bindiga Gadan-Gadan A Jihar Katsina

Kowane Lokaci daga yanzu cikin makon nan, Jami’an tsaro a jihar katsina zasu kaddamar da wani sumame na hadin gwiwa akan ‘yan ta’adda da suka addabi jihar.

Sumamen na hadin gwiwa  zai kunshi  jami’an  ‘yansanda  sai  sojojin kasa  dana  sama da  kuma  jami’an tsaro  na farin kaya, da dai sauransu.

Kazalika rahotanni  sun baiyana cewar  za’a yi aiki  ne  tare da  jami’an sintiri  da aka  yiwa  rijista, Kamar yadda mai magana da yawun  rundunar  ‘yansandan  jihar  ASP Aliyu  Abubakar  ya  tabbatar da hakan.

A yan kwanakin nan dai,  Yan ta’adda  sun kara tsananta kai hare-hare  a jihar ta Katsina, Musamman garuruwan dake  kan iyakokin jihar  da  Zamfara da kuma Kaduna.