On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Yansanda Biyu A Jihar Imo

‘Yan bindiga sun harbe wasu jami’an yansanda guda biyu tare da wani Matashi har lahira, a yayin wani hari da suka kai wata Mahadar kan titi dake karamar hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar Imo.

Maharan sun bude  wuta batare da  kakkautawa ba a lokacin da suka je wurin  da jami’an tsaro ke tsayawa domin bincike ababen hawa.

Shaidun gani da ido da suka bukaci a sakaye sunansu  sun fadawa manema Labarai cewar, Wani mutum ya gamu da ajalinsa  sakamakon wani  harsashin bindiga  da  ya same shi.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar yansandan jihar  ASP Henry Okoye, Ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya  ce  a yanzu haka an fara  farautar  yan bindigar.