On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Bindiga Sunyi Barazanar Halaka Jaririn Da Wata Mata Ta Haifa A Hannunsu A Jihar Kaduna

YAN TA'ADDA

Yan bindigar da suka sace wadansu mata Ukku yan uwan juna a jihar Kaduna, wadanda suka hada da wata mai tsohon ciki wadda ta haifi jaririnta a hannun yan bindigar, sunyi barazanar halaka matan da suke tsare dasu.

Kazalika sunyi  barazanar  halaka jaririn da matar  ta Haifa, muddin  danginta  suka kasa biyan naira milyan  50 nan da kwanaki biyu masu zuwa.

An  sace d  matan ‘yan uwan juna su ukku a ranar  17  ga  watan Yulin bana a gidansu dake  Mando a jihar Kaduna, a lokacin da suke kula da lafiyar mahaifiyarsu wadda take  fama da rashin lafiya.

Dangin matan da aka sace sun baiyana cewa  abunda suka iya hadawa kawo  yanzu shine naira milyan  6 da rabi daga cikin makudan kudin da  ‘yan bindigar suka neman.

Kazalika shima dan uwan matan mai suna Kabir Yusuf, Lokacin da yake ganawa da manema Labarai a Kaduna, Ya roki gwamnatin jihar  da kuma  sauran yan kishin kasa  dasu  temaka masu, domin ceto  rayukan bayin Allah.