Kotu ta Hukunta Bankuna, Gidajen Mai Kan Take Dokokin Muhalli
Kotun Tafi-da-Gidanka ta REMASAB Ta Hukunta Total Energies, MRS, A.A. Rano da Sauran Masu Laifin Keta Dokokin Tsaftar Muhalli.
Gasar Cin Kofin Duniya: Argentina Ta Sha da Kyar a Hannun Masar
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Argentina ta yi babban abin mamaki bayan ta farfado daga ci 2-0 da Masar ke yi mata, ta kuma yi nasara da ci 3-2 domin tsallakawa zuwa zagayen ukun karshe tare da cigaba da raya burin Lionel Messi, na sake lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya.
Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci ICPC Ta Gudanar da Binciken Gaggawa
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da ta gudanar da cikakken bincike kan hukumar nan bawa shugaban kasa shawara kan al'amuran kasashen waje (PFIPC), wadda ake zargin ta bogi ce kuma tana amfani da sunan Fadar Shugaban Ƙasa ba tare da sahalewa ba.
ICPC Ta Kama Likitan El-Rufai Kan Zargin Take Umarnin Kotu
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta sanar da kama Farfesa Bello Abubakar, likitan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, bisa zargin bayar da bayanan ƙarya bayan wata ziyarar duba lafiya da kotu ta amince a yi wa tsohon gwamnan yayin da yake tsare a hannun hukumar.
Da Dumi-Dumi: Sanarwar Infantino Kan Dakatarwar da Aka Yiwa Dan wasan Amurka
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, Giani Infantino ya magantu akan zargin da ake yi na cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya taka rawa akan dakatar da jan katin da aka yiwa dan wasan kasar Amurka, Folarin Balogun.
Gwamnatin Tarayya ta Bukaci 'Yan Jarida su Daina Yada Aiyukan 'Yan Ta'adda
Gwamnatin Tarayya ta bukaci 'yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta da su hana 'yan bindiga da 'yan ta'adda samun farfagandar da suke nema, tana mai cewa aikin jarida mai ɗa'a da ƙwarewa na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma yaƙi da tsattsauran ra'ayi.
Amurka ta Fice Daga Gasar Kwallon Kafa ta Duniya Duk da Katsalandan da ake Zargin Trump Da Yi
Belgium ta nuna ƙarfin wasa inda ta lallasa Amurka da ci 4-1 a wasan zagaye na biyu na Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 da aka buga a filin wasa na Seattle.
Mbappe Ya Soki Sanatar Paraguay Kan Kalaman Wariyar Launin Fata
Jagoran cikin fili na kungiyar kwallon kafa ta ƙasar Faransa, Kylian Mbappe, ya bayyana wata Sanata daga Paraguay, Celeste Amarilla, a matsayin wadda ba ta cancanci muƙaminta ba, bayan ta yi masa kalaman wariyar launin fata a shafukan sada zumunta sakamakon wasan zagaye na biyu na Gasar Kofin Duniya da Faransa ta doke Paraguay da ci 1-0.
Gwamnatin Kano ta Fara Sabunta Taswirar Kano a Karon Farko Bayan Shekaru 30
Gwamnatin Jihar Kano ta fara aikin sake sabunta tsarin birnin Kano wanda ya shafe fiye da shekaru 30 ba tare da an yi masa cikakkiyar bibiya ba, tare da rufe gine-gine sama da 200 da aka gina ba bisa ka'ida ba cikin wata guda.
© Copyright 2026 Steam Broadcasting and Communications Limited. Powered by Aiir.