Oloyede Ya Miƙa Ragamar Shugabancin JAMB
Farfesa Is-haq Oloyede ya miƙa ragamar shugabancin Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ga Farfesa Segun Aina, wanda ya zama sabon magatakardar hukumar.A wajen bikin miƙa mulki, Oloyede ya gode wa ma’aikata da masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka ba shi, yana mai bayyana wa’adinsa na shekaru goma a matsayin lokaci na sauye-sauye, gaskiya da bunƙasa hukumar. Sabon magatakardar, Farfesa Segun Aina, ya yi alƙawarin kare martabar JAMB, inganta ayyukanta da kuma amfani da fasaha domin ƙara inganci da gaskiya wajen gudanar da ayyukan hukumar. Aina ya karɓi ragamar shug
NLC Ta Yi Bayani Kan Jinkirin Albashin Kano
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano ta buƙaci ma’aikatan gwamnati da jinkirin albashi ya shafa da su kwantar da hankalinsu, tana mai cewa matsalar ta samo asali ne daga tangarɗar fasaha da bankin da ke kula da biyan albashin ya fuskanta.
Atiku Ya Soki Kalaman Tinubu Kan Rayuwar Najeriya
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (ADC), Atiku Abubakar, ya soki kalaman Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa rayuwar al’ummar Najeriya na ci gaba da inganta.
© Copyright 2026 Steam Broadcasting and Communications Limited. Powered by Aiir.