Majalisar Dattawa ta Bukaci a Mutunta Bukatar Iyalan Mary Habila na Binne Yar su Cikin Sirri
Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sunday Katung, ya bukaci al'umma su kwantar da hankalinsu tare da mutunta bukatar iyalan marigayiya Mary Habila bayan rasuwarta a gidan ministan aiyuka na tarayya, Dave Umahi.
Wani Yankin Kwara ya Rubatawa Tinubu Wasika Kan Tabarbarewar Tsaro
Al'umar yankin Lata Nna dake karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara sun rubutawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wasikar neman daukin gaggawa akan matsalolin garkuwa da mutane, yanta'adda da kuma kashe-kashe da ya addabi su.
ADC ta Caccaki Manufofin Tattalin Arzikin Tinubu
Jam'iyyar ADC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da manufofin tattalin arzikin da ta bayyana a matsayin masu jefa 'yan Najeriya cikin talauci, ko kuma ya sauka daga mulki, tana mai cewa al'umma ba za su iya cigaba da jure wahalhalun da suke fuskanta ba.
Atiku ya Soki Gwamnatin Tinubu akan Yadda Take Kashe Kudaden Kasa
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sama da naira biliyan 210 da aka cusa sau biyu a kasafin kudin 2026 ya nuna gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na cikin gwamnatocin da suka fi yin wakaci ka tashi da dukiyar kasar nan.
Mbappe Ya fi Kowa Kwallaye a Gasar Kwallon Kafa ta Duniya
Dan wasan gaba na kasar Faransa, Kylian Mbappé, ya kafa sabon tarihi bayan ya zama wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin gasar cin Kofin Duniya ta FIFA, inda yawan kwallayensa ya kai 22.
© Copyright 2026 Steam Broadcasting and Communications Limited. Powered by Aiir.